Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU), ta zargi jiga-jigan yan siyasar Najeriya da kwashe kudaden kasarnan gabanin babban zaben 2023 maimakon magance matsalolin da ke addabar ilimi a kasar.

Shugaban kungiyar ASUU, reshen jami’ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole ne ya bayyana hakan, inda ya kara da cewar gwamnati ta koma tattaunawa da kungiyar duk da cewar sabanin yarjajeniyar farko ne.


A cewarsa, gwamnati da ASUU za su duba daftarin yarjejeniyar 2009 wacce tawagar gwamnati ta fara tare da ASUU a 2007 kuma aka kammala shi a watan Mayu, 2021
Idan dai za a iya tunawa, ASUU ta ci gaba da koka kan cewar Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da daftarin yarjejeniyar na tsawon watanni 9, saboda haka kungiyar ta nisanta kanta da duk wata tawagar Gwamnatin Tarayya da ta sake kafawa domin bude wata tattaunawar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.