Korea ta Arewa ta kara azama wajen shirin inganta makamanta a cikin wannan shekarar, duk kuwa da cewa tana fama da takunkuman karayar tattalin arziki.
Babban hafsan hafsoshin sojin Korea ta Kudu ya ce sun gano makamai masu linzami 8, masu cin gajeren zango da Korea ta Arewa ta harba a tekun gabashi na kusa da Japan.

Japan ta tabbatar da lamarin, inda ta ce Korea ta Arewa ta yi gwajin makamai masu linzamin ne a yankuna da dama, tana mai cewa kasar ta yi gwaje gwaje da dama na makamai a wannan shekarar fiye da yadda ta taba yi.
