Shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya ce ba su ji dadin kalaman ba musamman daga Tinubu da ake kira jagoran jam’iyyar.
Ya ce kuskure ne ya ambaci shugaba Buhari a wurin da baya nan.
Daga baya Tinubu ya fito ya ce ba a fahimci kalamansa ba ne, yana mai cewar yana matukar mutunta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kuma ba zai taba raina shi ba.
Amma Shugaban jami’yyar na APC Abdullahi Adamu ya bayyana kalaman na Tinubu a matsayin “kururuwa bayan yaƙi” yana mai cewar kamata yayi yaje ya baiwa shugaba muhd Buhari hakuri.