Mazabar majalisar dattawa ta Sokototo ta Kudu ta kunshi kananan hukumomi bakwai da suka hadarda Bodinga, da Dange/Shuni,da Kebbe, da Shagari, da Tambuwal, da Tureta, da kuma Yabo.
A makon da ya gabata ne gwamnan ya janyewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Abuja.
A baya Gwamna Tambuwal ya wakilci mazabar Tambuwal/Kebbe a majalisar wakilai, inda ya zama shugaban majalisar a zangonsa na uku.
Gwamnan na Neman kujerar Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu,wanda Mohammed Danbaba, wanda kwanan nan ya fice daga PDP zuwa APC.