Dakarun runduna ta musamman ta Operation hadin kai sune suka kai a kauyukan Amdaga,da Balazola,da Ndakaine, daJango, da Sabah da kuma Gobara,duk a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Baya ga kashe ‘yan ta’adda 14 a yayin samamen, sun kama 15 daga cikinsu,tare da ceto iyalai 100 da suka hadarda mata 33 da yara 67.
Daraktan yada labarai na ma’aikatan tsaron kasar, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka a yayinda yake jawabi ga manema labarai a game da ayyukan sojin da ke gudana a yankin arewa maso gabashin Najeriya a tsakanin 19 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni.
Dakarun gwamnatin sun kuma kwato wata mota kirar Toyota Hilux, wanda ta kasance mallakin hukumar gyaran hanyoyin jihar Borno ce, ta ‘yan ta’addan suka karbe a tsohuwar hanyar Marte a cikin watan Fabrairu.