Ana fargabar cewar mutane da dama sun mutu sakamakon wani fashewar wani abu da aka samu a wata mujami’a dake garin Owo a Jihar Ondo a lokacin da Kristoci ke gabatar da ibada.

Bayanai sun ce wani abin fashewa mai kama da bam ya tashi a harabar mujami’ar ta St Francis dake kusa da fadar Basaraken garin, ‘Olowo na Owo’, abinda ya sa mutane tserewa domin tsira da rayukan su.


Ya zuwa wannan lokaci babu wani karin haske daga bangaren gwamnatin jihar ko kuma jami’an tsaro akan sanadiyar hadarin da kuma adadin mutanen da suka jikkata, sai dai shaidun gani da ido sun ce mutane da dama sun mutu, yayin da wasu kuma suka jikkata.


Sai dai wasu kafofin yada labarai sun ce ‘Yan bindiga ne suka kai harin kuma sun kashe mutane akalla 50 lokacin da suka bude wuta akan masu ibada da kuma wadanda ke wucewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *