Kungiyar ta musanta zargin da ake mata na hannu a harin ne a wasu takardu data rika rabawa matafiya a kan Babbar Hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua.
Takardun da kungiyar ta raba sun nuna cewa manufar Ansaru ita ce kare Musuluncui daga abin da ta kira, “Zaluncin gwamnatin Najeriya da sauran kasashen Afirka bakar fata.”

Wani shugaban matasa a yankin Birnin Gwari da ya bukaci a boye sunansa ya ce ’yan kungiyar sun yi ta raba takardun ne ga matafiya da sauran matane a kan babbar hanyar a ranar Alhamis da yamma
Takardun sunce babu ruwan akidar kungiyar da kai wa mutane da ba su ji ba, ba su gani ba hari babbar manufarta ita ce kare addinin Islama da Musulumi da aka zalunta ko aka ha’inta.
Kungiyar ta kuma karyata wani mai suna Abu Barra da da ke ikirarin cewa shi ne shugabanta, inda ta ce nan gaba za ta sanar da shugabanta.
Tun a ranar 17 ga watan Afrilu wani shafin Facebook da ake zargin na dan kungiyar Ansaru ne, ya karyata rahotannin da ke alakanta kungiyar da harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris, 2022.