Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa na jami’yyar, Asiwaju Bola Tinubu, ya sanar da cewar duk yadda sakamakon zaben fidda gwanin jam’iyyar ya kasance zai karbe shi hannu biyu.

Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya sanar da hakan ne yayinda yake jaddada cewar yana matukar mutunta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma girmama shi.


Wannan dai ya biyo bayan wasu rahotanni da ke yaduwa kan cewa Tinubu yayi bugun kirji a furucin da ya yi dangane da nasarar da Buharin ya samu a zaben 2015.


Tinubu ya bayyana hakan ne a masaukin shugaban kasa a birnin Abeokuta na Jihar Ogun, yayin da yake tattaunawa da daliget din APC gabanin zaben fitar da gwani na jam’iyyar da za a gudanar a makon gobe.


Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a mai dauke da sa hannunsa, Tinubu ya ce ba zai taba yin wani abu da zai lalata alakar siyasarsa da shugaban kasar ba.


Tsohon gwamnan na Legas ya ce jawabin da ya yi a Abeokuta a lokacin da ya gana da wakilan Jihar Ogun,yace abokan adawarsa ne suka sauya wa labarin fuska.


Ya ce furucin da ya yi a Abeokutan tunatarwa ce da kuma fatan hakan zai gamsar da shugaban kasar wajen kawar da duk wata adawa kan muradinsa dangane da zaben fidda gwanin da ke gabatowa na jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *