Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta fitar da jerin ka’idojin daza ayi amfani dasu wurin aiwatar da zaben 2023 na kasa da ke karatowa.

Kamar yadda ka’idojin suke wajibi ne shugaban akwatin zabe, PO ya kirga yawan takardun zaben wadanda suke dauke da hatimin hukumar.


Kan batun amfani da wayoyi yayin zabe, kamar yadda dokokin suka nuna, wajibi ne kawar da duk wata waya ko na’urar da za’a iya amfani da ita wurin daukar hotuna a harabar zabe.


Dokar ta tabbatar da cewar ba za ayi amfani da sakamakon wani akwati ba wanda yawan kuri’u ya zarce yawan masu zaben da aka tantance, kuma wajibi ne jami’in da ke da alhakin tattara kuri’u ya bayar da rahoto idan hakan ta faru.


Haka zalika tazarar da ke tsakanin ‘yan takara biyu wadanda suka fi yawan kuri’u kamar yadda dokar ta tanadar, ba yawan masu zaben da suka karbi katinan zabensu ba ne (PVCs) a wurin zaben da aka dage zabe, ko aka rushe shi ko kuma ba a gudanar da shi ba kamar yadda sashi na 24(2 & 3), sashi 47(3) da sashi 51(2) na dokar zaben 2022 ya tanadar.


Wajibi ne baturen zabe ya dakata har sai an gudanar da zabe a akwatinan kuma an tattaro sakamakon a cikin fom din da ya dace sannan a gabatar da shi.


A cewar Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya gabatar da wadannan jerin dokokin ne a Abuja yayin wani taro na musamman da aka yi da Kwamitin tuntubar kungiyoyi akan tsaron zabe don tabbatar da tsaron zaben gwamnonin da za a yi a jihar Ekiti.


Yakubu ya ce gabatar da ka’idojin na nuna cewa hukumar ta kammala duk wasu shirye-shiryen aiwatar da zabe a akwatina.


Yayin da ake kokarin kafa dokar zaben 2022, ya ce wajibi ne hukumar ta sake duba dokokin zaben da za su taimaka wurin aiwatar da zabe mai zuwa lafiya.


A cewarsa, da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara), dokokin zabe na 2022 da kuma ka’idojin aiwatar da zaben sune hanyoyin daza ayi amfanu dasu wurin shirya babban zabe mai karatowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *