Hukumar Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta sanar da ranar Alhamis 9 ga watan Yuni, a matsayin ranar da za’a fara jigilar alhazai daga Najeriya zuwa Kasa Mai Tsarki.

Shugaban Hukumar NAHCON, Hassan Zikrullah ne ya sanar da hakan a lokacin taron sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar alhazan tsakanin hukumar da kamfanonin jiragen sama da aka bai wa aikin, ranar Juma’a a Abuja.


Ya ce Hukumarsa ta turawa Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya bukatar karin kujerun aikin Hajji ga Najeriya, kuma hukumar tasa tana jiran amsa.


Ya bayyana cewar rukunin farko ta jami’an hukumarsa zasu bar Najeriya zuwa kasar Saudiyya a ranar Litinin 6 ga watan Yuni, domin tarbar alhazai daga ranar Alhamis 9 ga watan Yuni.


A cewarsa, an sanyar 9 ga watan Yuni domin fara jigilar ne tare da bayar da isasshen lokacin kammala shirye-shiryen jigilar maniyyata daga Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *