Ƙungiyar kare al’adun Fulani a Najeriya ta Miyetti Allah ta ce an kashe makiyaya aƙalla mutane 10,000 tare da raba wasu miliyan biyu daga muhallansu a faɗin ƙasarnan cikin shekara bakwai da suka wuce.

Sun bayyana hakan ne bayan wani taro kan tsaro da ƙungiyar ta shirya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Northern Consensus Movement (NCM) ta ‘yan Arewa sakamakon matsalolin tsaro da suka ce Fulani na fuskanta.


Cikin wata sanarwar bayan taro a ranar Juma’a, ƙungiyar ta ce daga 2015 zuwa yanzu makiyaya da dama sun fuskanci matsaloli, inda aka sace ko kashe dabbobi fiye da miliyan huɗu.


Ana yawan zargin wasu ‘yan ƙabilar Fulani da aikata fashi da garkuwa da mutane musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya, abin da shugabanni da ƙungiyoyin ƙabilar ke musantawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *