Shugaban kasar Amurka Joe Biden zai kai ziyara kasar Saudiyya, a wani mataki da ake ganin abin mamaki saboda ya taba yin kira da a mayar da kasar saniyar ware.

Kasar Saudiyya  jim kadan bayan da Amurka ta shigar da bukatu na ganin ta kara yawan gangar man da ake fitarwa tare da taka muhimiyar rawa wajen ganin an cimma batun tsagaita wuta tsakanin bangarori masu yaki a Yemen,a haka a cewar fadar shugaban kasar Amurka.


Amurtka nada kyakyawar hulda da Saudiyya a fanonin da suka jibanci tattalin arziki,da kuma tsaro.


Kafofin New York Times da Washington Post da CNN, hade da waso kafofin sadarwa sun tabbatar da cewar Biden zai kai ziyara Saudiya tare da ganawa da Yarima mai jiran gadon sarautar kasar Mohammad Bin Salman da ake zargi da hannu a kisan dan jaridan nan Jamal Khashoggi a shekarar 2018 a ofishin jakadancin Saudiyya dake Turkiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *