Shugaba Joe Biden na Amurka ya bukaci da’a hana sayar da makamai ko bindigogi da mutane kan kai hari da su.

Shugaba Joe Biden na Amurka ya bukaci da’a hana sayar da makamai ko bindigogi da mutane kan kai hari da su, bayan harin da wani ɗan bindiga dadi ya kai wanda ya hallaka mutane da dama a wata makarantar firamare a Texas.


A wani jawabi da ya gabatar mai sosa zuciya cikin alhini daga fadarsa ta White House, Shugaban ya ce har “sai an kashe mutane nawa ne za’a dauki mataki.


Biden ya nemi da a ƙara yawan shekarun da kaidar daya kamata mutum ya kai kafin a sayar masa da bindiga da kuma tsananta bincike ga duk wanda zai sayi makami.


Sannan ya bukaci a sake tsarin kariyar doka da masu ƙera bindiga suke da shi.


Biden ya ce an samu raguwar ta’addar harbin mutane da yawa a lokaci guda, bayan da ‘yan majaliar dokokin Amurka na jamiyu biyu na Democrat da Republican suka hada kai suka yi dokoki masu tsauri na mallakar bindiga a 1994.


Shugaban ya ce a yanzu bindiga ce lamba ɗaya wajen hallaka yara a Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *