Wannan wani ɓangare ne na soma aiwatar da dokar haramta a-caɓa a birnin Jihar.
A watan da ya gabata aka bijiro da dokar kuma ta soma aiki a wannan satin a wani yunƙuri na ƙarawa jihar tsaro.

Wannan ba shi ne karon farko da gwamnati ta kakaba wannan haramci ba.

A Janairun 2020, gwamnati ta haramta hawa babura a wasu ƙananan hukumomi 15 na Jihar.
Wasu dai na nuna shaku kan ko dokar za ta ɗore, ganin alfanunsu da yanayin cunkoson a birni.