Kakakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya gana da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan,a ranar Alhamis a Abuja.

Malam Shehu ne ya bayyana haka a wani rubutu da ya yi a shafinsa na dandalin sada zumunta Twitter, tare da tura Hotonsa tare da tsohon shugaban ƙasar.


Kakakin shugaban ƙasa Buhari na ɗaya daga cikin mutanen da suka ɗauka da zafi kan Jonathan a farkon wa’adin wannan gwamnatin.


A wancan lokacin, Shehu ya zargi tsohon shugaban ƙasan da laifin tsaikon da aka samu na jinkirin shugaba Buhari gabanin naɗa mambobin majalisar zartarwa a gwamnatinsa.


Shehu ya ce Kwamitin karɓar mulki bai samu cikakken haɗin kai daga gwamnatin Jonathan ba kuma hakan ya shafi sabuwar gwamnatin shugaba Buhari.
Sukar tsohon shugaban ta ragu yayin da Goodluck Jonathan ya fara ɗasawa da shugaban ƙasa Buhari.


An jima ana alaƙanta Jonathan da shiga tseren takarar shugaban ƙasa karkashin jami’yyar APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *