Gwamnatin tarayya ta haramta sayar da naman daji a matsayin matakin kariya domin daƙile yaɗuwar cutar ƙyandar biri.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan cibiyar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta ce mutum shida sun kamu da ƙyandar biri a Najeriya a watan Mayu, kuma mutum ɗaya ya mutu sakamakon cutar.


Kyandar biri, cutar da ƙwayoyinta ba su da ƙarfi, na yaɗuwa a Najeriya a yankunan ƙauye, musamman inda suke da matsanancin zafi.


An taɓa samun ɓullar cutar a 2017.


Dabbobin da kan iya yaɗa cutar sune nau’ukan su ɓera da zomo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *