Daga yanzu za’a rika kiran Turkiyya da Türkiye a Majalisar Dinkin Duniya bayan ta samu sahalewar hakan daga Ankara.

An tambayi kasashe da dama kan sauyin sunan, a wani bangare na sauye-sauyen da shugaban kasar ke neman kawowa tun a bara.


Türkiye zaifi dadi idan aka kira kasarsu da shi, yafi daidai da al’adar mutanenmu, wayewarsu da kuma kimar da suke da ita,a cewar shugan kasar turkiyya Racep Tayyip Erdogan a watan Disamba.


Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta sauya sunan nan take a wannan makon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *