Al’ummar Musulmi mazauna Jihar Anambra sun yi wata ganawa da gwamnan jihar, Farfesa Chukuma Soludo, bayan kisan gillar da aka yi wa wata mata Musulma da ‘ya’yanta hudu a jihar, abinda ya jawo Allah-wadai daga ko ina a kasarnan.

A wani sakon da ya saka a shafinsa na Twitter Gwamna Soludo ya ce ganawarsa da Shugabannin Musulmin Anambra ta yi matukar wayar masa da kai Sarkin Hausawan Awkan.

Ya kuma ce gwamnan Jihar ta Anambra ya yi musu alkawarin tura karin jami’an tsaro zuwa yankunan da al’ummar Arewacin Najeriya ke zama.


Yace Gwamna Soludo ya bukaci su cigaba da zama da yin sana’o’insu a cikin Jihar kamar yadda suka saba, kamar yadda ‘yan kabilar Igbo da ke zaune a arewacin Najeriya ke ci gaba da zamansu lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *