A wannan juma’ar mamayar da Rasha take yiwa Ukraine ta cika kwana dari daya cif.

Da ya ke gabatar da jawabi kamar yadda ya saba ta bidiyo ga majalisar dokokin Luxembourg, a daren ranar Alhamis, Shugaban Ukraine ya ce, yanzu dakarun Rasha sun kwace kusan kashi ɗaya bisa biyar na ƙasar.


Volodymyr Zelensky, ya ce kusan sojojin Ukraine 100 ne ke mutuwa a kullum, a kokarin da suke na hana Rasha dannawa ta kama iko da ƙarin yankunan gabashin Ukraine din.


Wani babban janar, Olexiy Gromov, ya ce babu bukatar dakarunsa suja baya daga Severodonetsk, duk da cewar Rasha na kokarin yi musu kawanya.


Shugaba Zelensky ya jaddada cewar, samun ƙarin makamai daga ƙasashen Yamma, zai sauya yanayin yakin, Ukraine ta rika samun nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *