Mutumin mai suna Tanko Rossi Sabo, ya wallafa a shafinsa na Facebook yada ya gabatar da kuɗin naira miliyan 12 domin a rabawa maɓukata a karamar hukumarsa.
Daga cikin abubuwan da aka yi da kuɗin akwai sayen rigunan jerseys da biyan kuɗin makaranta da asibiti ga mutane. Ya kuma raba sauran kuɗaɗen ga magoya bayansa.
Mista Tanko ya ce ko wacce irin muhawara ko suka da za a tafka bai dame shi ba, tunda dai duk abin da ya samo ya dawo gida ya sanya farin ciki a fuskokin al’ummarsa.
Tanko Rossi na cikin delegates din Kaduna da suka halarci taron PDP na kasa inda aka gudanar da zabe da tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takara a PDP.