Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ce bom din ya tashi da ’yan ta’addan ne a kan titin Eke Ututu zuwa Orsu da ke Karamar Hukumar Orsu ta Jihar Imo a ranar Laraba.
Kakakin Rundunar Sojin Kasa Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ne ya sanar a Enugu a ranar Alhamis cewa bom din ya yi wa ’yan ta’addan munanan raunika.
A karshe ya roki al’ummar yankin Kudu maso Gabashin Najeriya masu son zaman lafiya da su sanar da sojoji kan wuraren da suke zargin akwai abubuwan fashewa domin su kwance su,”