Kungiyoyin magoya bayan mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, sun yi fatali da yunkurin yin sulhu wajen fitar da dan takarar jam’iyyar.

Kungiyoyin, wadanda ke karkashin NYPT da TSO, sun ce ya kamata a saka wa tsohon Gwamnan na Jihar Legas saboda irin rawar da ya taka wajen yin nasarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a 2015.

Da suke karanta matsayin kungiyoyin a wani taron manema labarai a Abuja, jam’ian kungiyoyin, Abdullahi Tanko Yakasai da Aminu Suleiman, Yakasai, sun roki Shugabancin jam’iyyar karkashin Sanata Abdullahi Adamu da ya bari a fafata a zaben.


A cewar Abdullahi Yakasai, muddin APC na son ta ci gaba da rike mulki a 2023, ya zama wajibi ta gudanar da sahihin zaben dan takararta.
Ya kuma yi kira ga daliget din jam’iyyar da kada su yarda su karbi kudi daga ’yan takara don sayar da kuri’unsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.