Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta ja hankalin ’yan Najeriya kan alfanun hawa keke musamman a bangaren lafiyar jiki.

Kwamandan hukumar na Jihar Kogi, Stephen Dawulung, ne ya yi jan hankalin, ta bakin Jami’in Ilimantarwar Hukumar, Ayodeji Oluwadunsin.


Sanarwa dai an fitar da ita ne a shirye-shiryen hukumar na gudanar da bikin zagayowar Ranar Keke ta Duniya ta 2022, da za a gudanar ranar 3 ga watan Yunin da muke ciki.
Taken bikin na bana dai shi ne ‘Hawa keke domin inganta muhalli da zamantakewa’.


Haka zalika ya ce yanzu haka hukumar tayi yarjejeniya da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Duniya domin fara shirye-shirye, da ayyukan da za su dawo da amfani da Keke a Najeriya, a matsayin hanyar sufurin da za ta maye gurbin wadanda ake amfani da su a yanzu.


Ya ce dogaro motoci da babura, ya sanya ’yan Najeriya da ke rayuwa a birane ke fama da matsalar tashin farashin man fetur da dangoginsa, wanda hakan ke kara yawan man da kasar ke bukata, ga kuma cunkoson ababen hawa da ya ki karewa.


Don haka ya ce hukumar na fatan hadin guiwar da ta yi da kungiyar mahaya keke ta Jihar Kogi, da sauran masu ruwa da tsaki, na yin zagaye kan Kekunan zai inganta hanyar sufurin da kuma sauya tunanin al’umma a kai.


Sai dai Stephen ta bakin Ayodeji ya gargadi mahaya keken da su bi dokokin hanya kamar sauran masu abin hawa saboda lafiyar kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *