Gwamnatin Tarayya ta ce tana ɗaukar matakan shawo kan hauhawar farashin kayan masarufi a sassan ƙasar, inda yanzu haka take shirin taro na kasa kan matsalar.

Gwamnati ta ce za ta bijiro da matakai masu karfi domin tabbatar da habbakar wasu ɓangarori na masana’antu a ƙasar da ke fuskantar matsalolin ci gaba.


Ministan Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed da ke shaida haka a lokacin taron majalisar koli ta kasa a Abuja, ta ce suna son ganin cewa cikin gaggawa sun shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyakin abinci, da bijiro da hanyoyin samawa ƙasar mafita da sauƙin rayuwa tsakanin al’umma.


Ta kuma ƙara da cewa nan bada jimawa ba za su sanar da wasu tsare-tsaren rage raɗaɗin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *