Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Dr Ahmad Gumi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da ma’aikatar da za ta dinga kula da lamurran makiyaya don kawo karshen matsalolinsu.
Ya fadi hakan ne yayin jawabi ranar Laraba a taron makiyaya da bada tsaro ga Fulani wanda ya gabata na kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya da kungiyar sasanci ta arewa suka gabatar a Abuja.

Haka zalika, shugaban kungiyar MACBAN, Husseini Bosso ya koka a kan irin kalubale da suke fuskanta a harkar noma da kiwonsu amma duk da haka gani ake kamar su ne ke da alhaki a ta’addanci bayan su yafi shafa.
Kungiyar Miyetti Allah ta makiyayan shanu da Kungiyar Sulhu ta arewa (NCM) ne suka shirya taron.
A cewar malamin, makiyayan fulani da sauran kungiyoyin sun cancanci kula irin wacce ake bawa yan Neja Delta