Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da shugabanni da mambobin jam’iyyar a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Obi, wanda a kwanakin baya ya yi murabus daga babbar jam’iyyar adawa, ya ce PDP ta sauka daga turbar sa’a da nasara bayan ta ki mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin Kudu.

Da yake magana ta bakin Darakta Janar na yakin neman zabensa, Dakta Doyin Okupe, Obi ya caccaki jam’iyyar PDP da rashin adalci ta hanyar yin watsi da tsarin shiyya-shiyya na jam’iyyar.
A cewarsa, wadanda ke adawa da tsarin shiyya-shiyya a jam’iyyar PDP sun durkusar da wanzuwar ta tare da karya yarjejeniyar shugabannin da suka kafa jam’iyyar,