Dan takarar PDP a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar yana la’akari da Rt. Hon. Emeka Ihedioha a sahun abokan takararsa a 2023.

Rahoton yace ana maganar Atiku Abubakar zai iya dauko tsohon mataimakin shugaban majalisa, Emeka Ihedioha
Hon. Emeka Ihedioha ya zama mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayyar kasar nan a lokacin da Aminu Waziri Tambuwal ya rike majalisa.

Ana kyautata zaton Aminu Waziri Tambuwal ya kawowa ‘dan takarar shugaban kasar wannan shawara cewa ya tafi da ‘dan shekara 57 a zaben 2023.

Sannan Ihedioha ya na cikin wadanda suka matsawa Gwamnan Sokoto ya hakura da neman tutar PDP na shugaban kasa, ya janyewa Atiku Abubakar.


An rawaito cewa ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP sun shirya zaben Aminu Tambuwal a matsayin ‘dan takara domin yana tare da tsohon gwamnan jihar.

Wata majiya ta shaida cewa bangaren Gwamnan na Sokoto sun ba Atiku sunan Ihedioha.
Da farko ana zargin ‘dan takarar bai gamsu da wannan zabin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *