Lauyan ya nemi Alkali ya hana jam’iyyar PDP tsaida Atiku Abubakar takara a duk wani zaben Najeriya.
Jideobi ya na ikirarin Atiku ba cikakken ‘dan Najeriya ba ne, don haka bai cancanta da mukami ba.
A karar da ya shigar a kotun da ke zama a garin Abuja, Jideobi ya hada da Atiku Abubakar, jam’iyyar PDP, hukumar INEC da babban lauyan gwamnati.
Mai karan ya ce kyale wanda ake tuhuma (Atiku Abubakar) ya shiga zaben 2023 a matsayin ‘dan takara, yana nufin jam’iyyar PDP ta sabawa dokokin Najeriya.
Hakan zai ci karo da sashe na 1(1) & (2), 25 da 131(a) na kundin tsarin mulkin 1999 a cewar Lauyan.
Har ila yau, Lauyan ya ce a doka, nauyi yana kan hukumar INEC na ganin cewa ba ta bar wani wanda ba mutumin Najeriya ba ya samu iko da gwamnatin kasar.