Wani dan majalisar dattawa daga jam’iyyar APC mai mulki ya ce kamata ya yi jam’iyyarsu ta tsayar da wani daga kudancin kasar.

Yayin da babban jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar da dan arewa a zaman dan takararta na shugaban kasa, wani dan majalisar dattawa daga jam’iyyar APC mai mulki ya ce kamata ya yi jam’iyyarsu ta tsayar da wani daga kudancin kasar.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce bai wa yankin kudanci takarar shi ne babban alheri da adalci ga APC , kuma a cewarsa zai sa ta ci zabe a 2023.

Wannan na zuwa ne, yayin da rahotanni ke cewa akwai zaman dar-dar a jam’iyyar ta APC gabanin zaben fid da dan takarar shugaban kasa.

Bayan shugaba Muhammadu Buhari ya tara gwamnonin jam’iyyarsu, tare da shaida musu cewa ya zabi wanda zai gaje shi kuma yana son su goya masa baya domin ya samu tikitin tsayawa takara, abin da aka ce bai yi wa wasu gwamnonin dadi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *