Al’ummar yankin Birnin Gwari sun ce tun da hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ta zama tarkon mutuwa to sun yanke shawarar kauracewa hanyar baki daya har sai mahukunta sun dauki mataki.

A ranar Talata ne dai ‘yan bindiga su ka datse jerin gwanon motocin matafiya da su ka taso daga Birnin Gwari zuwa Kaduna inda su ka fasa tawagar sannan su ka kone motoci takwas da kuma sace mutane da dama.

Dan-masanin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Idris Abdurra’uf, ya ce mafi akasarin wadanda aka sace mata ne da yara da kuma dalibai masu jarabawa kuma an shiga da su daji.


Alhaji Zubairu, ya kara da cewa daga ranar Laraba kar wanda ya bi wannan hanya daga Birnin Gwari zuwa Kaduna har sai an ga an dauki mataki na tabbatar da tsaro a kan wannan hanya kuma jama’a za su samu wata hanya da za su bi.


Daya daga cikin matafiyan da su ka tsira Haruna Abubakar ya ce ‘yan bindigar sun yi musu kofar rago sai da suka shiga suna tafiya bisa jagorancin ‘yan banga ashe suna da yawa sai da suka fada gaba daya inda motoci uku ne kadai su ka samu damar dawowa da baya.


Haruna ya kara da ce har yanzu ba a iya tantance ko mutane nawa ne aka yi awon gaba da su ba kuma muddin ba a kawo karshe wannan fitina ba to garin Birnin Gwari zai iya dai-dai-cewa.


Gwamnatin jahar Kaduna dai ta tabbatar da faruwar wannan hari kuma kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Malam Samuel Aruwan, ya ce gwamnati na kokari wajen kawo karshen matsalar tsaro a jihar baki daya.


Ya ce matsalar ta tsaro ba abu ne da gwamnati ke bi da sanyin jiki ba, amma jami’an tsaro suna iya bakin kokarin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *