Alamu na nuna cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai nemi takarar Sanata na mazabar kudancin jihar Sokoto a zabe mai zuwa na 2023

Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto bayan kusan mako daya kenan da Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya janye neman takarar shugaban kasa.


A tsakiyar shekara mai zuwa wa’adin Gwamnan na Sokoto zai cika, zai sauka daga karagar mulki
Wannan ta sa Aminu Waziri Tambuwal ya fara hangen yin takarar Sanata a karkashin jam’iyyar PDP, zai karbe tikiti ne daga hannun Aminu Bala Bodinga.
Tsohon kwamishinan na gidaje da safayo na jihar Sokoto, Aminu Bala Bodinga shi ne wanda ya samu nasarar lashe zaben fitar da gwani na PDP na Sanatan.


Tun a baya an yi tunanin Aminu Bodinga ya rike tikitin ne kafin ganin yadda sakamakon zaben fitar da gwanin shugaban kasa zai kasance a jam’iyyar PDP.


Ganin Tambuwal bai yi nasara ba, Bodinga zai iya ba Mai gidansa wuri ko kuma jam’iyyar ta gudanar da wani sabon zaben fitar da gwani na Sanata.


Rahoton ya nuna Bodinga yana cikin manyan na-kusa da Tambuwal a siyasa. Tun 2015 ya ke tare da Gwamnan a lokacin yana ‘dan majalisa na Bodinga.


Bayan Rt. Hon. Tambuwal ya fice daga APC zuwa PDP a 2018, Bodinga yana cikin wadanda suka biyo shi. A 2019 ya nada shi kwamishina bayan fadi zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published.