Tsohon gwamnan Kano da take takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ya so tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya yi masa mataimaki a takararsa ta shugaban kasa.

Sanata Kwankwaso ya ce lokacin da Peter Obi ya fice daga PDP ya so a ce ya shiga sabuwar jam’iyyar da ya kafa wato NNPP domin su yi takara tare.

Tsohon gwamnan da ke wadannan kalamai a tattaunawarsa da kafar Talabijin ta Channels a Najeriya, ya ce a mako mai zuwa za su gudanar da zaɓen fitar da gwani na takarar shugaban kasa, duk da cewa shi kaɗai ne ke takarar.


Sai dai ya ce a yanzu NNPP za ta yi kokarin farautar wani fitacce daga Kudancin Najeriya domin su yi takara tare na neman tikitin shugaban kasa a zaɓen 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published.