Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ba zasu ba Ukraine makamai masu linzami da za su iya shiga yankin Rasha ba.


A cewar Kamfanin dillacin labarai na Reuters, shugaban na Amurka bai bayyana makaman da yake nufi ba, amma ya ce taimakon soji ga Ukraine ba zai shafi yadda za ta yi aiki da su ba.

Ukraine ta sha rokon ƙasashen yammci makamai masu cin dogon zango.

A can baya rahotanni sun ce gwamnatin Biden tana tunanin ba Ukraine manyan makamai.
Rasha ta yi gargadin cewa ba Ukraine manyan makamai zai kara rura wutar rikici.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *