Shan Taba Sigari na yin sadaniyar rasa rayukan ‘yan Najeriya dubu 29 a kowacce shekarar.

Yayin da a yau ake gudanar da bukukuwan yaki da busa taba sigari ra duniya, wata kungiyar kula da lafiya a Najeriya ta ce, akalla mutane dubu 29,000 ke mutuwa kowacce shekara sakamakon illar busa tabar.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka kiyasta cewar, hukumomin lafiyar kasar na kashe akalla Naira biliyan 526 kowacce shekara domin kula da masu cututtukan da ke da nasaba da busa tabar.


Kungiyar ta ce, wadannan kudaden da ake kashewa tamkar barnatar da tattalin arzikin Najeriya ne kuma gwamnatin kasar kashi 10 kacal take karba daga kamfanonin tabar sigari.


Bayanai sun nuna cewa, ana ci gaba da samun karuwar masu zukar sigari a nahiyar Afrika, yayin da Najeriya ke ci gaba da shigo da tabar daga kasashen duniya 44.


Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Afrika da su sanya harajin muhalli kan kamfanonin sarrafa sigari saboda yadda suke gurtaba muhallin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *