Idan baku manta ba,a karshen makon nan ne jami’an hukumar yaki da hana cin hanci da rashawa ta kasa EFCC sukayi dirar mikiya a gidan Okorocha kana suka tafi dashi.
Bayan haka, aka ce an gurfanar dashi a gaban kotu, amma batun belinsa ya ci tura saboda wasu dalilai.

A rahoton baya-bayan nan, an ce daga karshe an ba da belinsa.
Belin nasa na zuwa ne daidai lokacin da jam’iyyar APC ke ci gaba da tantance ‘yan takarar shugaban kasa da suka sayi fom kwanan nan.
Okorocha na daga cikin wadanda za a tantance a yau Talata, kamar yadda wani jerin sunayen wadanda za a tantance a ranar ya nuna.