Yan ta’addan da suka kai wa jirgin kasan Kaduna hari sun kara sati biyu a kan wa’adin barazanar halaka fasinjoji 62 da har yanzu suke hannunsu yau.

‘Yan ta’addan da suka kai wa jirgin kasan Kaduna hari sun kara sati biyu a kan wa’adin barazanar halaka fasinjoji 62 da har yanzu suke hannunsu yau.

Sai dai, sharadin jinkirin shi ne: Wajibi ne gwamnatin tarayya ta sakar musu yaransu takwas dake hannunsu kafin ko ranar 13 ga watan Juni daga nan ne za a cigaba da maganar sakin fasinjoji 62.

A ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan ta’addan suka halaka fasinjoji tara gami da garkuwa da mutane da dama bayan lalata jirgin kasa a wani kilomita kadan daga Kaduna, babban birnin jihar Kaduna.

Daga bisani sun sako wasu daga ciki, tare da barin 62 a hannunsu.

Wani mawallafi mazaunin Kaduna, Tukur Mamu, ya bayyana karin mako daya na wa’adin ranar da masu garkuwa da mutanen su ka yi a Talatar da ta gabata.

Mamu, wanda kuma shi ne mai magana da yawun fitaccen malamin addinin musuluncin da ya dade yana jawo cece-kuce, Sheikh Ahmad Gumi, wanda bai ce uffan ba a lokacin da gwamnatin tarayya tayi awon gaba da kananan yaran ‘yan ta’addan takwas.

Mamu ya ce ya yi nasarar rarrashin ‘yan ta’addan har suka jinkirta wa’adin kwanakin da suka bayar bayan an gano inda yaran nasu suke tare da taimakon hukumomin tsaro na jihar Adamawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *