Yayin wata hira da gidan talabijin na Faransa, Mista Lavrov ya ce shugaban na Rasha yana bayyana a bainar jama’a kowace rana, kuma babu wani mai hankali da zai ga alamun rashin lafiya tattare da shi.

Ana ci gaba da samun rade-radin da ba a tabbatar da ke cewa Mista Putin wanda ke shirin cika shekaru saba’in a karshen wannan shekara, na fama da rashin lafiya, watakila ma ciwon daji.