Okorocha, wanda a halin yanzu ya ke wakiltar mazabar Imo ta yamma a majalisar dattawa, an gurfanar da shi gaban mai shari’a Inyang Ekwo a ranar Litinin.

Ana tuhumarsa da laifuka 17 da suka hada da damfara kudi da ta kai N2.9 biliyan wanda hukumar EFCC ta shigar a kansa.