Gwamnatin Brazil tace adadin mutanen da suka mutu sakamakon ruwan saman da aka shatata makon jiya ya kai 79, yayin da wasu da dama suka bata.

Gwamnatin Brazil tace adadin mutanen da suka mutu sakamakon ruwan saman da aka shatata makon jiya ya kai 79, yayin da wasu da dama suka bata.

Ministan kula da ci gaban yankuna Daniel Ferreira ya shaidawa manema labarai cewar alkaluman da suka tattara sun tabbatar da mutuwar mutane 79.

Fereira yace, mutane da dama sun bace, kuma wasu 25 sun samu raunuka, yayin da 3,957 suka rasa muhallan su.

Ministan yayi gargadin cewar suna fuskantar Karin ruwan sama a yankin, saboda haka aka bukaci mutane su zauna cikin shirin ko ta kwana.

Wannan dai shi ne iftila’i na baya bayan nan a cikin jerin bala’o’i da suka hada da zabtarewar kasa da ambaliyar ruwa da suka haifar da matsanancin yanayi a Brazil.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *