Fadar shugaban kasa ta nesanta Mai girma Muhammadu Buhari da zargin ba Goodluck Jonathan takara a jam’iyyar APC a zaben 2023.

Wata majiya ta shaida cewa babu yadda za ayi shugaba Muhammadu Buhari ya goyi bayan Goodluck Jonathan ya zama ‘dan takaran APC.

Buhari wanda ya saba caccakar gwamnatin jam’iyyar PDP ba zai marawa jam’iyyarsa baya ta tsaida wanda shi da kan sa ya tika shi da kasa a 2015 ba.

Majiyar ta shaida cewa hadiman tsohon shugaban kasar ne suke yada jita-jitar, su na nuna hotunan mai gidan na su tare da Muhammadu Buhari.

Wani lokaci mutanen Jonathan su ka yi ta yama-didi da hotunan Goodluck Jonathan a duk lokacin da ya ziyarci shugaban Najeriyan ko na kusa da shi.

Duk da Buhari bai fadawa Duniya matsayarsa a kan wanda ya kamata ya gaji mulki a hannunsa ba, wani da ke Aso Villa ya ce babu Jonathan a lissafinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *