Dan takarar jam’iyyar (PDP) a zaben gwamnan jihar Borno na 2023, Mohammed Jajare, ya zargi gwamnan jihar, Babagana Zulum na baiwa abokai, iyalai da yan uwansa kwangiloli ta hanyar fakewa da aiki kai tsaye.

Jajare ya kuma yi zargin cewa gwamnan na siye manyan yan PDP a jihar don kawar da adawa a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi, Jajare ya bayyana cewa tsawon shekaru gwamnati mai ci a Borno ta fitar manyan masu fada aji daga PDP don ci gaba da tsarin jam’iyya daya a jihar.

Ya ce da wannan zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP da aka yi cikin gaskiya da amana wanda ya samar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin gwaninta jam’iyyar za ta tabbatar da sukar manufofin gwamnatin APC idan ba zai amfani mutanen Borno kamar yadda yake a kundin tsarin mulki.

Ya ce idan aka zabe shi a matsayin gwamna a 2023, zai dawo da dukkanin ma’aikatan gwamnati da aka sallama sannan ya biya su hakkinsu da aka tauye tsawon shekaru.

A cewarsa, yanayin rashin tsaro a jihar ya kawo wahalhalu da bai kamata ace an yanke ma’aikata daga inda suke samun kudin shiga ba bayan an hana su zuwa gonaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *