A yau Litinin Jam’iyyar APC mai mulkin kasa za ta soma tantance masu neman takarar shugaban ƙasa inda ake sa ran kai har gobe Talata ana gudanar da tantancewar.

Jumullar mutum 23 ne ake sa ran cewa za su halarci tantancewar.

Rahotanni na cewa ana sa ran tantance mutum 11 a yau Litinin, sa’annan kuma sauran 12 kuma a gobe Talata.

Wannan duk na zuwa ne bayan da jam’iyar ta APC ta ɗage zaɓen fitar da gwanin da ya kamata ta gudanar 29 da 30 ga watan Mayu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *