Yau 29 ga Watan Mayun 2022 saura shekara daya dai dai Shugaban kasa muhammadu Buhari ya bar Ofis a matsayin Shugaban kasa tare da Mika mulkin ga Wanda yayi Nasara a Zaben badi.

Wasu rahotanni da jaridun Kasar Nan duka wallafa ya nuna cewa , Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar mulkin Najeriya ba tare da kammala ayyuka da dama da ya dauko ba wasu Kuma baa farasu ba tun bayan alkawarin yinsu a shekarun baya .

Babban aiki na baya bayan Nan shine shimfida titim Jirgin Kasa daga Nan Kano zuwa Katsina ya tsaya a Maradi dake Jamhoriyar Nijar.

A Watan Fabareru na shekarar 2021 Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin ,Wanda yayi alkawarin cewa zaa kammala aikin a Watan Mayun shekarar 2023.

An shirya cewa zaa kashe sama da dala miliyan dubu 1 da dala miliyan dari 9 a aikin .

Sai Kuma shimfida bututun iskar Gas daga Ajakuta zuwa Kaduna zuwa Nan Kano Wanda shima Rahotanni ke cewa ko Rabin aikin baayi ba.

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya karbi mulkin Najeriya ne a ranar irin ta yau 29 ga Watan Mayun shekarar 2015 bayan ya kayar da tsohon Shugaban kasa Good luck Ebele Jonathan maici a wancan lokaci Wanda yau Shugaba Buhari ke cika shekara 7 akan Mulki.

A yanzu dai masana na ta kiraye kiraye ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi duk Mai yiyuwa wajen ganin anyi Zaben gaskiya a shekarar 2023 Wanda hakan zai iya cigaba da fito da martabar Najeriya a idanun duniya .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *