Buhari: “Za mu tabbatar da ƴan ƙasa sun zaɓi wanda suke so”.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada buƙatar tabbatar da mulkin dimukuradiyya a Afirka a taron Tarayyar Afirka da aka gudanar a birnin Malabo na Equatorial Guinea.

Shugaban ya ce, ba ƴan ƙasa damar zaɓar wanda suke so, shi ne ƙarfafa dimokuradiyya da zai bayar da damar gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da kuma mutunta zaɓinsu.

Shugaban ya faɗi haka ne a tattaunawar da ya yi da shugaban Malawi Lazarus Chakwera a gefen taron Tarayyar Afirka na musamman a Malabo babban birnin Equatorial Guinea a ranar Juma’a, kamar yadda fadar shugaban na Najeriya ta bayyana a cikin wata sanarwa.

Buhari ya ce Najeriya ba za ta ba Afirka kunya ba a babban zaɓen ƙasar da ke tafe, yana mai cewa dole ne shugabannin siyasar Afirka su mutunta ƴancin ƴan ƙasa na zaɓar wanda suke so.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *