Zaben fidda gwanin PDP: Ba zan daga wa kowa kafa ba, Gwamna Bala Mohammed.

Gwamnan jihar Bauchi kuma dan takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP, Bala Mohammed, ya ce bai shirya janyewa saboda kowanne dan takarar PDP ba.

Gwamnan ya bayyana matsayarsa ne yayin tattaunawa da Arise TV a ranar Asabar kan yuwuwar bayyanar dan takarar yarjejeniya daga arewa maso gabashin kasar nan a gagarumin taron zaben fidda gwanin da ake yi a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.

Ya ce:

“Ba zan daga wa kowa kafa ba. Ba shugaban kasan arewa maso gabas zan zama ba, shugaban kasar Najeriya zan zama. Babu wanda zan bi baya cikin ‘yan takara na arewa maso gabas. Kalla duk abubuwan da nayi. Na bi tudu, na bi gangare. Na fahimci banbance-banbance.

“Kuma daga daya bangare na mutanen kasar nan da ke Kudu, ku yarda da ni, saboda abinda na yi na kwazo, abubuwan da nayi a babban birnin tarayya, Bauchi da ko na. Don haka. babu wanda zia zo ya ce in daga wa wani kafa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *