Ukraine ta ce dole ne sojojinta su ja da baya daga sansaninsu na karshe a Luhansk da ke gabashin kasar idan har ana son su kaucewa fadawa hannun Rasha.

Jami’ai sun ce sojojin Rashar sun shiga birnin Severodonetsk amma har yanzu sojojin Ukraine na dakile hare-harensu Donetsk da Luhansk.

A yayin jawabinsa na dare, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce Ukraine za ta yi tsayin daka wajen kwato yankin Donbas.

Kyiv na ci gaba da yin kira ga kawayenta na kasa da kasa da su samar mata da karin kayan aikin soji domin tunkarar hare-haren na Rasha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *