Tsohon Ministan sufurin kuma dan takara shugaban kasa a jamm’iyyar apc e Rotimi  Amaechi ya nisanta kansa daga duk wata tuhuma na wasosso da kudin jihar Rivers a lokaci daya shugabanci jihar

Tsohon Ministan sufurin kuma dan takara shugaban kasa a jamm’iyyar apc dake tafe Rotimi  Amaechi ya nisanta kansa daga duk wata tuhuma na wasosso da kudin jihar Rivers a lokaci daya shugabanci jihar.


A jiya juma’a ne kotun daukaka karar tayi watsi da bukatar tsohon ministan daya taba rike mukamin Gwamna a Ribers,wanda gwamnati mai ci yanzu haka a karkashin gwamna Nyesom Wike ta kafa wani kwamitin da zai gudanar da bincike akan wasu daga cikin hada-hadar kudade ba bisa ka’ida ba da ake zargin Rotimi Amaechi.

Takkadama na zafi tsakanin Rotimi Amaechi da Gwamnan yankin Rivers Nyesom Wike,wanda ya bukaci a gudanar da bincike biyo bayan gano wata hada hada ba bisa ka’ida ba, da Rotimi Amaechi yayi a lokaci da yake rike da mukamin gwamnan jihar.

Tsohon Ministan na ci gaba da nisanta kansa daga duk wata badakala,a cewarsa ana neman shafa masa kashin kaji ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *