Shugaban kasa Muhd Buhari ya bayyana ilimi a matsayin abinda ke samar da cigaba a kowace ƙasa yana mai cewar gwamnatinsa ta himmatu don ganin ta kara rage adadin yaran da basa zuwa makaranta.

Shugaban kasar ya sanar da hakan ne yayin bikin zagayowar ranar yara ta duniya tare da matasan Najeriya, inda yayi alkawarin cewar gwamnatinsa zata cigaba da aiki tukuru domin ganin kowane yaro ya samu ilimi, wanda hakan zaisa su samu kyakkyawar makoma.

Cikin Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar tace, Shugaban ya amince da matsayin ilimi a cikin cigaban kowace ƙasa kuma ya himmatu don ganin an ƙara raguwar adadin yaran da basa zuwa makaranta.

Ya kara da cewar yayinda ilimin yaran Najeriya zai cigaba da kasancewa kan gaba a wannan gwamnati, sauran batutuwa kiwon lafiya, kariya daga cutarwa, muggan kwayoyi, kungiyoyin asiri, fataucin yara da cin zarafi suna samun kulawar da ake bukata daga gwamnati.

Shugaba Buhari yayi imanin cewar yaran Najeriya sun cancanci kasa mai mai kwanciyar hankali inda zasu iya girma, yin abokai, mu’amala da tafiye-tafiye cikin lumana, sannan su zama shugabanni masu nasara a fannoni daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *