Jam’iyyar APC mai mulkin kasarnan ta dage taron zaben dan takarar shugaban kasarta zuwa ranar Litinin 6 ga watan Yuni, 2002

Sakataren Yada Labaran APC na Kasa, Barista Felix Morka ya ce, sabanin kwana biyu da jam’iyyar ta shirya gudanar da taron a baya, yanzu taron zai gudana ne a cikin kwana uku, dagar ranar Litinin 6, ga watan yuni zuwa Laraba, 8 ga watan Yuni, 2022.

Sanarwar tace sakamakon karin wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) tayi na mika sunayen ’yan takarar jam’iyyu, jam’iyyar APC ta sanar da dage babban taronta na zaben dan takarar shugaban kasa data shirya a ranar Lahadi 29 zuwa Litinin 30 ga watan Mayu, ya koma daga ranar Litinin 6 zuwa Laraba, 8 ga watan Yuni, 2002.

Ya sanar da hakan ne a jajibirin ranar taron, wanda da farko jam’iyyar ta shirya gudanarwa ranar Lahadi, 29 zuwa Litinin 30 ga watan Mayu, 2022.

Hakan na zuwa ne a ranar da babban jam’iyyar adawa da PDP zata fara gudanar da nata taron a Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *