Hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa INEC ta tsawaita lokutan zabe tare da kara lokacin zabukan fitar da gwani.

Hukumar INEC ta kara tsawaita lokacin ne bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyyun siyasa 18 da aka yiwa rijista.

A yayin taron wanda aka gudanar a hedikwatar INEC a Abuja, kwamitin bada shawarwari tsakanin jam’iyyu ya nemi a kara wa’adin mako guda ga jam’iyyun domin kammala zabukansu na fidda gwani.

Shugaban kwamitin Injiniya Yabagi Yusuf Sani ne ya nemi INEC ta dage ainihin lokacin data sanya na farko na ranar 3 ga watan Junin gobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *